TARIHIN SARAUNIYA AMINA ZARIYA
TELBIJIN KAI TSAYE BATUTUWA AMSOSHIN TAKARDUNKU Tarihin Amina sarauniyar Zazzau 23.03.2009 Taƙaitaccen tarihin rayuwar Amina sarauniyar Zazzau Tambaya: Fatawar farko a shirin namu ta fito daga hannun malama Maimuna Yakubu Nuhu daga Jihar Gombe a tarayyar Najeriya. Malamar cewa ta yi; Ku ba ni tarihin rayuwar Amina sarauniyar Zazzau wato “Queen Amina”, a ina ta rasu, kuma a ina kabarinta yake a halin yanzu. Shin akwai sauran zuriyarta kuwa a ƙasar Zazzau. Amsa: To dangane da wannan tambaya, mun tuntuɓi Ahmad Adamu, masanin tarihi a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya a Najeriya. Adamu: Amina Sarauniyar Zazzau, wadda ta rayu daga shekarar 1533 zuwa 1610, ɗaya ce daga cikin ‘ya'ya biyu da sarkin Zazzau Bakwa Turunku ya haifa. Wato ita Amina ɗin da kuma ƙanwarta mai suna Zariya. Ta yi sarautar Zazzau bayan rasuwar mahaifinta, daga shekara ta 1509 zuwa 1522, wato shekarunta 13 ke nan akan karagar mulki. Kuma ita ce mace ta farko da ta mulki masarautar Zazzau, kuma ta shida a cikin s...