Posts

Showing posts from May, 2025

MAKANCEWAR TINIBU

Image
 Jinkirta Jana'iza Ba Zai Tayar da Matattu Ba: Darasin Jonathan da Makancewar Tinubu BARR SOLOMON DARLUNG Babu wani shugaban kasa a tarihin Najeriya da ya samu goyon bayan neman tazarce kamar Goodluck Jonathan. 'Yan siyasa daga kowane bangare, gwamnoni, sanatoci, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, attajirai, da sama da kungiyoyin goyon baya 10,000 masu karfi da kudi sun mamaye kafafen watsa labarai kullum, suna tabbatar da nasararsa—wasu har kafin karfe 12 na rana a ranar zabe. A zamanin gwamnatin Jonathan, kudi ba matsala ba ce. Ana wulwula su babu tunani, duk wanda ya nuna goyon baya yana samu. Har abin ya kai, kawai ka gaishe “Mama Peace” da “Ina kwana,” za ka samu ruwan kudi. Wata guda kafin zaben Fabrairu 2015, gwamnatin Jonathan ta boye ta dauko kwararren mai binciken ra’ayi daga kasa da kasa domin tantance sakamakon zabe. Abin mamaki, binciken ya nuna cewa idan aka gudanar da zabe a lokacin da aka tsara, Jonathan zai fadi. A gigice, shugaban ya kira NSA Sambo Dasu...

BOKO HARAM SUNKASHE KAFTIN DIN SOJOJI A WANI MUMMUNAN HARIN DA SUKAKAI A KARAMAR HUKUMAR GWAZA

Image
  An kashe wani Kaftin Sojoji da Soja guda a lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari a garin Izge da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno da sanyin safiyar Laraba. Mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce ‘yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe 1 na safe amma jami’an tsaro sun dakile harin. “Wani Kyaftin da Soja daya ne suka rasa rayukansu, amma sojojin mu, Civilian JTF, mafarauta, da ‘yan banga sun kashe ‘yan ta’adda uku, suka gudu suka bar makamai da babura sama da 10,” inji shi. Sarkin ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma godewa Gwamna Babagana Zulum bisa taimakon jami’an tsaro. Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta karfafa sojoji da fasahar yaki na zamani. Harin dai ya biyo bayan wani lamari makamancin haka da ya faru a garin Buni Yadi na jihar Yobe, inda aka kashe sojoji hudu kwanaki kadan bayan da gwamnonin Arewa maso Gabas suka yi wani taro kan dabarun tsaro. Trust Tv

Back in History: PRESIDENT UMARU MUSA YAR'ADUWA died today, 15 years ago (15 May 2010). He was the second Head of Nigeria to die at Aso Rock Villa after General Abacha who died in the same villa in 1998. Yaradua was critically ill and was first flown to Wiesbaden in Germany where he had always received treatment but later moved to Saudi Arabia. In Saudi his health condition did not improve. He was from there flown back to Nigeria to be treated at home in the Villa. Not long thereafter, His Excellency Umaru Yaradua passed on to the great beyond. He was flown to his home State of Katsina where he was buried in line with the tenets of his faith, Islam. He was survived by his dearly beloved wife, Turai and numerous children. Nigerians remember him as an honest President who played little of politics in any decision he took. He was a President who preferred to work for national interest. #EndBadGovernanceInNigeria #viralpost2025シ2025 #viralpost2025シ

Image
 Back in History: President Umaru Musa Yaradua died today, 15 years ago (15 May 2010). He was the second Head of Nigeria to die at Aso Rock Villa after General Abacha who died in the same villa in 1998.  Yaradua was critically ill and was first flown to Wiesbaden in Germany where he had always received treatment but later moved to Saudi Arabia. In Saudi his health condition did not improve. He was from there flown back to Nigeria to be treated at home in the Villa. Not long thereafter, His Excellency Umaru Yaradua passed on to the great beyond.  He was flown to his home State of Katsina where he was buried in line with the tenets of his faith, Islam. He was survived by his dearly beloved wife, Turai and numerous children.  Nigerians remember him as an honest President who played little of politics in any decision he took. He was a President who preferred to work for national interest. #EndBadGovernanceInNigeria #viralpost2025シ2025 #viralpost2025シ

YAN BINDIGA SUN FATATTAKI SOJOJI A ZAMFARA

Image
  'Yan bindiga a Arewa maso Yamma sun fatattaki sojoji daga sansanin sojojin Najeriya a Zamfara. Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun mamaye sansanin sojojin Najeriya da ke jihar Zamfara tare da saka musu wuta, lamarin da ya sanya ake fargabar za a yi asarar rayuka.