BOKO HARAM SUNKASHE KAFTIN DIN SOJOJI A WANI MUMMUNAN HARIN DA SUKAKAI A KARAMAR HUKUMAR GWAZA

 An kashe wani Kaftin Sojoji da Soja guda a lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari a garin Izge da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno da sanyin safiyar Laraba.


Mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce ‘yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe 1 na safe amma jami’an tsaro sun dakile harin. “Wani Kyaftin da Soja daya ne suka rasa rayukansu, amma sojojin mu, Civilian JTF, mafarauta, da ‘yan banga sun kashe ‘yan ta’adda uku, suka gudu suka bar makamai da babura sama da 10,” inji shi.

Sarkin ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma godewa Gwamna Babagana Zulum bisa taimakon jami’an tsaro. Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta karfafa sojoji da fasahar yaki na zamani.

Harin dai ya biyo bayan wani lamari makamancin haka da ya faru a garin Buni Yadi na jihar Yobe, inda aka kashe sojoji hudu kwanaki kadan bayan da gwamnonin Arewa maso Gabas suka yi wani taro kan dabarun tsaro.

Trust Tv

Comments

Popular posts from this blog

SHIRYE SHIRYEN TARON GONA FACEBOOK CONNECT 1:0

The Muslims in the Eastern part of Nigeria are facing existential threats from their fellow Igbos

An gudanar da gagarumin taron Gona facebook Connect.