SHIRYE SHIRYEN TARON GONA FACEBOOK CONNECT 1:0
Gona Facebook Connect 1.0 ta gudanar da ziyarce-ziyarce ga wasu masu riƙe da madafun iko a Gona.
Cigaba da ziyarce-ziyarce da Kwamitin Shirye-shiryen Gona Facebook Connect ta keyi ga masu ruwa da tsaki na kasar Gona, kwamitin ta kaiwa shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Akko (Hon. Baba S. Fulani) ziyara a Gidan sa dake Nan Gombe.
yayin ziyarar, wakilan kwamitin sun gabatar da jawabai akan makasudin wannan bikin da Kuma alfanun sa ga matasan kasar Gona Baki daya.
Hon. S. Fulani ya nuna farin cikin sa ga kwamitin tare tabbatar da goyon bayan sa dari bisa dari don ganin an gudanar da wannan Biki cikin farin ciki da walwala.
Gona Facebook Connect committee

Comments
Post a Comment