An gudanar da gagarumin taron Gona facebook Connect.


Da yammacin yau Lahadi 23/11/2025, Aka gudanar da gagarumin taron haɗin kan matasa masu hulɗa da kafafen saɗa zumunta musamman facebook.


Taron ya gudana ne a babban ɗakin taro dake International Hotel a chikin garin Gombe inda aka tara manyan sarakuna iyayen ƙasa, manyan yan siyasa, masu riƙe da madafun iko da Mallamai masana Addini harda na boko.


Mai martaba Uban ƙasa Alh. Umar Abdulkadir Abdulsalam (MNIM) shi ya kasance uban taron inda ya nuna jindaɗinsa ganin yadda matasa mabambantan ra'ayi, jami'ya, da kuma addinai suka haɗu guri guda domin ƙara ƙarfafa Alaƙa tsakanin juna da sada zumunci.


Ya ƙara da cewa irin wannan taro taro ne mai matukar muhimmanci a chikon Al'umma sannan zai ƙara kawo haɗin kai a ƙasar Gona fiyeda yadda ake tunani.


Mai girma Shugaban Ƙaramar hukumar Akko, Hon. Dalladi Adamu (Baraden Gona) shine ya kasance mai masauƙin baƙi a wannan babban taro inda ya miƙa godiyar sa ga ilahirin Alumar da suka halarci wannan taro mai Albarka sannan ya nuna jindaɗinsa da ƙara jaddada goyon bayansa akan wannan katafariyar Gidauniya ta Gona facebook Connect sannan yayi addu'a Allah ya maida kowa gidansa lafiya.


Dr. Adamu Ahmed Adam , Shugaban tsangayar koyarda ilimin halayyar Ɗan Adam (Sociology) a jami'a mallakar Jihar Gombe (Gombe State University) yayi ta'aliƙi akan abunda ya shafi zage zage da cin mutuncin juna a kafafen sada zumunta (Cyber Bullying) inda ya ja hankalin matasa da su gujewa zage zage da cin mutuncin juna domin Akwai hukuncin da doka ta tanadar musu.


Mal. Muawuya Muhammad Bello  (Wakilin mallaman Gona) ya fadakar da matasa kan kiyaye dokokin ubangiji a mu'amalarsu ta yau da kullum tsakaninsu da Al'umma. 


Shugaban Komitin Gona facebook, Hon. @Idris Abubakar ya nuna godiyarsa da jindadin akan yadda sarakuna iyayen ƙasa, Masu ruwa da tsaki, da manyan yan kasuwa harma da komitin gydanarwa suka bada goyon baya da gudumawarsu don ganin wanna taron ya gudana fiyeda yadda ake so.


Daga ƙarshe Kungiyar Gona Facebook Connect ta karrama mai martaba sarki da lamban ban girma (Award) bisa duba da ire iren Ayyukan Alkhairi da yake shimfiɗawa a wannan ƙasa ta Gona da ƙokarin haɗa kan Al'umma domin ingata tsaro da zaman Lafiya tsakanin Al'ummar ƙasar Gona.


✍️ Auwal Labaran Shehu 

Daraktan yaɗa labarai na Gona facebook Connect.

Comments

Popular posts from this blog

SHIRYE SHIRYEN TARON GONA FACEBOOK CONNECT 1:0

The Muslims in the Eastern part of Nigeria are facing existential threats from their fellow Igbos