ZA'A KARAMMA HON.AISHATU MB AHMAD CIKIN GWARAZAN DA SUKAYI FICE A AFRICA WAJEN TALLAFAWA HARKAR ILIMI.
ZA'A KARAMMA HON.AISHATU MB AHMAD CIKIN GWARAZAN DA SUKAYI FICE A AFRICA WAJEN TALLAFAWA HARKAR ILIMI.
Jaridar Sahel Reporters ta ruwaito cewa za'a karrama tsohuwar kwamishinan ilimin jihar Gombe Hon.Aishatu MB Ahmad da lambar yabo na musamman a matsayin wanda tayi fice wajen tallafawa harkar ilimi ga matasa(Pillar Of Educational Support for youth).
Hon.Aishatu MB Ahmad zata karbi lambar yabon ne ranar 3/11/2022 a babban dakin taro na Rotunda Conference Hall dake ma'aikatar kula da harkokin kasashen waje (Ministry Of Foreign Affair) anan babban birnin tarayya Abuja.
Ana saka ran cewa Hon.Aishatu MB Ahmad zata karbi lambar yabon ne yayin tsaka da taron ranar matasa na kasa na wannan shekarar ta 2022.
Shi wannan lambar yabo hadakar kungiyoyin matasa na kasa da kuma hadin guiwar majalisar matasa ta kasa (Nigerian Youth Parliament) sune sukayi aiki tukuru wajen zakulo Hon.Aishatu MB Ahmad a fadin Africa baki daya.
Muna Addu'ar Allah yasa ayi taro lafiya ,ya kara mata daukaka cikin dukkan lamuran ta .
*Ahmad Abdullahi Deputy l*✍️
(Nana Media Office)
1/11/2022.

Comments
Post a Comment