Da yammacin yau Lahadi 23/11/2025, Aka gudanar da gagarumin taron haɗin kan matasa masu hulɗa da kafafen saɗa zumunta musamman facebook. Taron ya gudana ne a babban ɗakin taro dake International Hotel a chikin garin Gombe inda aka tara manyan sarakuna iyayen ƙasa, manyan yan siyasa, masu riƙe da madafun iko da Mallamai masana Addini harda na boko. Mai martaba Uban ƙasa Alh. Umar Abdulkadir Abdulsalam (MNIM) shi ya kasance uban taron inda ya nuna jindaɗinsa ganin yadda matasa mabambantan ra'ayi, jami'ya, da kuma addinai suka haɗu guri guda domin ƙara ƙarfafa Alaƙa tsakanin juna da sada zumunci. Ya ƙara da cewa irin wannan taro taro ne mai matukar muhimmanci a chikon Al'umma sannan zai ƙara kawo haɗin kai a ƙasar Gona fiyeda yadda ake tunani. Mai girma Shugaban Ƙaramar hukumar Akko, Hon. Dalladi Adamu (Baraden Gona) shine ya kasance mai masauƙin baƙi a wannan babban taro inda ya miƙa godiyar sa ga ilahirin Alumar da suka halarci wannan taro mai Albarka sannan ya nuna jindaɗin...
Congrats
ReplyDelete