ANKADDAMAR DA KUNGIYAR GONA MILTARA PDP GRASSROOT MOBLIZATION
AN KADDAMAR DA KUNGIYAR GONA MILTARA PDP GRASSROOT MOBILIZATION
Da yammacin Jiya asabar ne manyan yan jam'iyyar PDP da matasa da mata suka halarci kaddamar da wannan kungiya mai suna a sama.
Wannan kungiya an kafata ne don wayar da kan al'umma akan kyawawan manufofi da tsare-tsaren jam'iyar PDP da kuma bada gudunmawa wa yan takarkarun PDP da kuma wayar da kan matasa kan zaben jam'iyyar PDP a kakan zabe mai zuwa na 2023.
A jawabin uban kungiyar ya nuna jin dadinsa da farin cikinsa na wannan kungiyar ganin yadda take da kyawawan manufofi da kuma tsayuwarta tsayin daka ganin jam'iyyar PDP ta samu nasara.
Sai jawabi na biyu daga bakin zababben shugaban kungiyar shima yayi jawabin nuna jin dadinsa tareda sanyawa kungiya albarka da nuna goyon baya dari bisa dari da yin aiki sau da kafa da wannan kungiya domin samun nasara.
Daga karshe a madadin shugabannin wannan kungiyar suna mika sakon godiya da ban gajiya mahalarta wannan taron musamman
Hon. Umar A adamu kalajanga
Hon. Musa shongo
Da sauran wadanda ban ambacesu anan ba.
Allah yabamu nasara.
Aliyu flavor PDP ambassador
Chairman garko youths PDP vanguard

Comments
Post a Comment