An fara Rushe Wajen ibadar Musulmai a Nigeria, Gwamnatin Legas ta rushe Masallacin Kasuwar Alaba Rago.
An fara Rushe Wajen ibadar Musulmai a Nigeria, Gwamnatin Legas ta rushe Masallacin Kasuwar Alaba Rago.
Wajan ibadar Musulmai a Nigeria yafara Fuskantar Barazana, Mazauna Babbar kasuwar Alaba Rago sun koka bayan zargin Gwamnatin jihar Legas da sanya wa a rushe babban Masallacin Kasuwar, wanda aka kashe Miliyoyin Nairori.
A baya-bayan nan ne Gwamnatin jihar ke ci gaba da rushe-rushe a cikin kasuwar, wanda hakan ya jawo asarar dukiya ga ‘yan kasuwar.
Sai dai a satin nan aikin ya biyo ta kan babban Masallacin Kasuwar Alaba, wanda yake ɗauke da bene. ‘Yan kasuwar na ci gaba da kokawa akan wannan mataki na Gwamnatin jihar.
Sai dai har yanzu babu cikakken bayani daga Gwamnatin jihar, kamar yadda mazauna kasuwar suka tabbatar.

Comments
Post a Comment