BAMU YADDA DA SABON SHUGABAN HUKUMAR INEC BA,SABODA BE YADDA DA HALACCIN NIGERIA AMATSAYIN KASA ME YANCI BA
AN BANKADO WASU SHARRI DA KAZAFI WANDA SABON SHUGABAN HUKUMAR ZABE INEC YAYIWA AREWACIN NAJERIYA
: Ga wasu daga cikin abubuwan da ake zargin sabon shugaban hukumar zabe ta kasa INEC Farfesa Joash Ojo Amupitan ya rubuta ya aike da shi Amurka a wajajen shekarar 2020, kamar yadda mai sharhi Bulama Bukarti ya bayyana a shirinsu na fashin baki:
1. Ya zargi ana yiwa Kiristoci kisan kiyashi
2. Ya zargi cewa yawan yan arewa da ake amfani da shi karya ne Arewa sun yi karin yawan mutanensu don kawai ace sun fi kowa yawa a Najeriya
3. Ya ce Hausa Fulani musamman Fulani yan kama waje zauna ne asalin Fulani ma ba kabila bace a Najeriya
4. Ya ce auren dole aka yiwa Najeriya, don kawai ayiwa wasu danniya da fin karfi
5. Ya ce hausa Fulani sun mamaye ko ina, aikin soja da sauran wajajen ayyuka da shuganci domin su mamaye komai
6. Ya ce Hausawa da Fulani sun mamaye Najeriya suna so sai sun musuluntar da Najeriya
7. Bai ma yarda da Najeriya ba sannan indai mutum ba kirista bane mabiyin darikarsa to ba halastacen mutum ko dan kasa bane da dai sauran kalaman kiyayya da ruruta wuta da yayi.
Da dai sauran munanan abubuwa da ya rubuta ya aikawa Amurka a lokacin bai san zai shiga Gwamnatin ba, bai san za a bashi mukamin shugaban hukumar zabe ba.
Yanzu wanda yake da wannan matsaya a zuciyarsa kuna ganin zai yi adalci a zabe ? Musamman zaben da akwai Musulmai da Kirista ko dan kudu da dan Arewa?
Yanzu dai an fara kiraye-kiraye ko dai ya sauka ko kuma Tinubu ya cire shi! Me zaku ce?
Follow Us => Muryoyi

Comments
Post a Comment